Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Al-Ahqaf — Ayah 29

46:29
وَإِذۡ صَرَفۡنَآ إِلَيۡكَ نَفَرٗا مِّنَ ٱلۡجِنِّ يَسۡتَمِعُونَ ٱلۡقُرۡءَانَ فَلَمَّا حَضَرُوهُ قَالُوٓاْ أَنصِتُواْۖ فَلَمَّا قُضِيَ وَلَّوۡاْ إِلَىٰ قَوۡمِهِم مُّنذِرِينَ ٢٩
Kuma a lõkcin da Muka jũya waɗansu jama'a na aljamiu1 zuwa gare ka sunã saurãren Alƙur'ãni. To, alõkacin da suka halarce shi suka ce: "Ku yi shiru." Sa'an nan da aka ƙãre, suka jũya zuwa ga jama'arsu sunã mãsu gargaɗi.
Footnotes
  • [1] Wannan yã nũna cewa a cikin aljannu akwai Musulmi da masu gargaɗi, kuma idan mutum ya yi gargaɗi, dõmin Allah, Allah zai taimake shi da mãsu saurãra masa, kõ da daga waɗansu jinsin da ba nãsa ba. Kuma zama a cikin wani addinin Allah da ya shige, ba ya isa ga wanda bai shiga addinin Musulunci ba, a bãyan bayyanar Musulunci.