Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Al-Fath — Ayah 20

48:20
وَعَدَكُمُ ٱللَّهُ مَغَانِمَ كَثِيرَةٗ تَأۡخُذُونَهَا فَعَجَّلَ لَكُمۡ هَٰذِهِۦ وَكَفَّ أَيۡدِيَ ٱلنَّاسِ عَنكُمۡ وَلِتَكُونَ ءَايَةٗ لِّلۡمُؤۡمِنِينَ وَيَهۡدِيَكُمۡ صِرَٰطٗا مُّسۡتَقِيمٗا ٢٠
Kuma Allah Yã yi muku wa'adin waɗansu ganĩmõmi mãsu yawa, waɗanda zã ku karɓo su, kuma Ya gaggauta1 muku wannan. Kuma Ya kange2 hannãyen mutãne daga gare ku, kuma dõmin ta kasance wata ãyã ce ga mũminai, kuma Yã shiryar da ku ga hanya madaidaiciya.
Footnotes
  • [1] Cin nasara makusanci, shĩ ne cin Haibara, a bãyan kõmawar Annabi Madĩna a ƙarshen zul Hajji. Sa'an nan ya fita wajen ƙarshen Muharram shekara ta bakwai. Aka samo ganĩma mai yawa. Waɗansu ganĩmõmi na waɗansu ƙasãshen da zã a ci a nan gaba har ƙarshen dũniya. Ganĩmar Haibara ita ce aka gaggauta.
  • [2] A lõkacin da Annabi ya fita daga Madĩna zuwa Hudaibiyya Allah Ya kange hannuwan Yahũdãwa daga iyãlan Musulmi na cikin Madĩna, in dã bã dõmin haka ba sai su je su fãɗa su da kashi da kãmu. Sai Allah Ya jefa tsõro a cikin zukãtansu.