Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Al-Fath — Ayah 24

48:24
وَهُوَ ٱلَّذِي كَفَّ أَيۡدِيَهُمۡ عَنكُمۡ وَأَيۡدِيَكُمۡ عَنۡهُم بِبَطۡنِ مَكَّةَ مِنۢ بَعۡدِ أَنۡ أَظۡفَرَكُمۡ عَلَيۡهِمۡۚ وَكَانَ ٱللَّهُ بِمَا تَعۡمَلُونَ بَصِيرًا ٢٤
Kuma Shĩ ne Ya kange hannayensu1daga gare ku, kuma da hannayenku daga gare su, a cikin Makka, bãyan Ya rinjãyar da ku a kansu. Kuma Allah Ya kasance Mai gani ga abin da kuke aikatãwa.
Footnotes
  • [1] Waɗansu Ƙuraishawa ne, sũ tamãnin, suka kewaye Musulmi a Hudaibiyya, da niyyar yaudara, sai aka kãme su, su duka, aka kai su ga Annabi, shi kuma ya yãfe musu, a bãyan ya nũna musu rinjãya. Wannan shĩ ne ya sabbaba yin sulhu.