Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Qaf — Ayah 30

50:30
يَوۡمَ نَقُولُ لِجَهَنَّمَ هَلِ ٱمۡتَلَأۡتِ وَتَقُولُ هَلۡ مِن مَّزِيدٖ ٣٠
Rãnar da Muke cẽwa ga Jahannama "Shin, kin cika?" Kuma ta ce: "Ashe,1 akwai wani ƙãri?"
Footnotes
  • [1] Wannan jawãbi na Jahannama yanã ɗaukar ma'anõni biyu. Ta farko tanã nũna ta cika ƙwarai, amma tanã kũkan a ƙara mata wani abu a cikinta. Wannan fassara ta yi daidai da ayãr da ta ce, "Lalle na cika Jahannama daga aljannu da mutãne gabã ɗaya." Sura ta 32, ãyã ta 13. Fassara ta biyu, ita ce Jahannama nã neman ƙãri tanã hushi sabõda mãsu sãɓawa umurnin Allah. Sũra ta 67 ãyõyi 6, 7 da 8.