Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Al-Hadid — Ayah 16

57:16
۞ أَلَمۡ يَأۡنِ لِلَّذِينَ ءَامَنُوٓاْ أَن تَخۡشَعَ قُلُوبُهُمۡ لِذِكۡرِ ٱللَّهِ وَمَا نَزَلَ مِنَ ٱلۡحَقِّ وَلَا يَكُونُواْ كَٱلَّذِينَ أُوتُواْ ٱلۡكِتَٰبَ مِن قَبۡلُ فَطَالَ عَلَيۡهِمُ ٱلۡأَمَدُ فَقَسَتۡ قُلُوبُهُمۡۖ وَكَثِيرٞ مِّنۡهُمۡ فَٰسِقُونَ ١٦
Shin, lõkaci bai yi ba ga wa ɗanda suka yi ĩmãnĩ1 zukãtansu su yi tawãlu'i ga ambaton Allah da abin da ya sauka daga gaskiya? Kada su kasance kamar waɗanda aka bai wa littãfi a gabãnin haka, sai zãmani ya yi tsawo a kansu, sabõda haka zukãtansu suka ƙẽƙashe, kuma masu yawa daga cikinsu fãsiƙai ne.
Footnotes
  • [1] Wanda yayi ĩmani da Allah amma bai bi umurninSa ba, sai zũciyarsa ta ƙeƙashe,ĩmãni ya fita sa'an nan kuma ya zama fãsiƙi mai fita hanyar gaskiya. Barin ciyarwa da dukiya dõmin jihãdi yanã nũna ƙeƙashħwar zũciya daga ĩmãni, sabõda haka faɗa da zũciya dõmin tsaron ĩmãninta shi ne jihãdi mafi girma.