Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Al-Mujadila — Ayah 14

58:14
۞ أَلَمۡ تَرَ إِلَى ٱلَّذِينَ تَوَلَّوۡاْ قَوۡمًا غَضِبَ ٱللَّهُ عَلَيۡهِم مَّا هُم مِّنكُمۡ وَلَا مِنۡهُمۡ وَيَحۡلِفُونَ عَلَى ٱلۡكَذِبِ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ ١٤
Ashe, baka ga waɗanda1 suka jiɓinci waɗansu mutãne da Allah Ya yi hushi a kansu ba, bã su cikinku, kuma bã su a cikinsu kuma sunã rantsuwa a kan ƙarya, alhãli kuwa sunã sane?
Footnotes
  • [1] Bãyan maganar mãsu tãyar da mutãne dõmin gãnãwa a cikin majalisa, sai kuma munãfikai mãsu mu'ãmala da kãfirai, kuma su je su zauna cikin majalisar Musulmi dõmin su ɗauki rahõtonsu zuwa ga maƙiyansu.