Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah At-Tahrim — Ayah 6

66:6
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ قُوٓاْ أَنفُسَكُمۡ وَأَهۡلِيكُمۡ نَارٗا وَقُودُهَا ٱلنَّاسُ وَٱلۡحِجَارَةُ عَلَيۡهَا مَلَٰٓئِكَةٌ غِلَاظٞ شِدَادٞ لَّا يَعۡصُونَ ٱللَّهَ مَآ أَمَرَهُمۡ وَيَفۡعَلُونَ مَا يُؤۡمَرُونَ ٦
Yã kũ waɗanda suka yi ĩmãni! Ku kãre wa kanku1 (da iyãlinku wata wuta makãmashinta mutãne da duwãtsu ne. A kanta akwai waɗansu malã'iku mãsu kauri, mãsu ƙarfi. Bã su sãɓã wa Allah ga abin da Ya umarce su, kuma sunã aikata abin da ake umarnin su.
Footnotes
  • [1] Tsare kai da iyãli daga wuta yanã sãmuwa da shiryar da su da karãtu da nasiha a kan addini. Wannan yanã a cikin kyawun zamantakewa wanda sũrar ke karantarwa.