Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Az-Zukhruf — Ayah 86

43:86
وَلَا يَمۡلِكُ ٱلَّذِينَ يَدۡعُونَ مِن دُونِهِ ٱلشَّفَٰعَةَ إِلَّا مَن شَهِدَ بِٱلۡحَقِّ وَهُمۡ يَعۡلَمُونَ ٨٦
Kuma waɗanda suke kira baicin Sa ba su mallaki cẽto ba, fãce wanda ya yi shaida da gaskiya, kuma sũ, sunã sane1 (da haka).
Footnotes
  • [1] Su waɗanda suka yi shaida da gaskiya sun san bãbu mai mallakar ceto ga wani fãce Allah. Sabõda haka Allah nã yi musu izni su ceci wanda Yake son su cece shi, ba wanda su suke so ba. Ma'anar iznin da ceto ga bãyin Allah sãlihai ita ce dõmin Allah Ya bayyana darajar mai ceton ne kawai, bã don yanã da wani hakki ba, ga Allah. Allah Ya tsarkaka daga wata halittar Sa ta sãmi wani hakki a kan Sa. Kõwa bãwan Sa ne.