Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Al-Hujurat — Ayah 1

49:1
يَٰٓأَيُّهَا ٱلَّذِينَ ءَامَنُواْ لَا تُقَدِّمُواْ بَيۡنَ يَدَيِ ٱللَّهِ وَرَسُولِهِۦۖ وَٱتَّقُواْ ٱللَّهَۚ إِنَّ ٱللَّهَ سَمِيعٌ عَلِيمٞ ١
Yã ku waɗanda suka yi ĩmãni! Kada ku gabãta (da kõme) gaba ga Allah da Manzon Sa.1 Kuma ku yi ɗã'ã ga Allah da taƙawa. Lalle Allah Mai ji ne, Masani.
Footnotes
  • [1] Wannan yã nũna mana cewa bã yã halatta ga Musulmi ya yi wani aiki ko ya faɗi wata magana sai yã san hukuncin Allah a cikinsu. Kuma kada ya ƙãra wãyõnsa a kan abinda Allah Yã ce, kuma kada ya rage idan yanã da ĩkon cikãwa. Dukan wannan yakan ja Musulmi ga ɓãcin ayyukansa, watau ya yi ridda daga Musulunci.