Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah At-Tur — Ayah 48

52:48
وَٱصۡبِرۡ لِحُكۡمِ رَبِّكَ فَإِنَّكَ بِأَعۡيُنِنَاۖ وَسَبِّحۡ بِحَمۡدِ رَبِّكَ حِينَ تَقُومُ ٤٨
Sai ka yi hakuri da hukuncin Ubangijinka, lalle kai fa kanã idãnun Mu, kuma ka tsarkake1 Ubangijinka da (tasbĩhi) game da gõde Masa a lõkacin da kake tãshi tsaye (dõmin salla kõ wani abu).
Footnotes
  • [1] (Ma'anar ita ce tsarkakewa kõ tasbĩhi, 'tsare sallõli, farillai, anã cewa' faɗin "Subhãnal lãhi wal Hamdu Lillãhi" a bãyan kõwane mazauni, dõmin ya zama kaffãrar wannan mazaunin.