Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Sad — Ayah 33

38:33
رُدُّوهَا عَلَيَّۖ فَطَفِقَ مَسۡحَۢا بِٱلسُّوقِ وَٱلۡأَعۡنَاقِ ٣٣
"Ku mayar da su a gare ni." Sai ya shiga yankansu1 da takõbi ga ƙwabrukansu da wuyõyinsu.
Footnotes
  • [1] Sulaimãna ya yanka dawãkin,dõmin kallonsu yã hana shi salla, wadda take farlu ainin ce a gare shi, amma tattalin kãyan yãƙi farlu kifãya ce. Anã gabãtar da farlu ainin a kan farlu kifãya. Wannan kuma ya nũna cewa anã cin dõki idan wani dalĩli bai hana ba. Dũbi Sũra ta 16, ãyã ta 8.