Abubakar Mahmood Jummi

Ayah by Ayah

Tags

Download Links

Abubakar Mahmood Jummi translation for Surah Sad — Ayah 34

38:34
وَلَقَدۡ فَتَنَّا سُلَيۡمَٰنَ وَأَلۡقَيۡنَا عَلَىٰ كُرۡسِيِّهِۦ جَسَدٗا ثُمَّ أَنَابَ ٣٤
Kuma lalle haƙĩƙa, Mun fitini1 Sulaiman kuma Muka jẽfa wani jikin mutum a kan karagarsa. Sa'an nan ya mayar da al'amari zuwa gare Mu.
Footnotes
  • [1] Wata rãna Sulaiman ya yi tunãnin ya sãdu da mãtansa ɗari uku, dõmin su yi cikunna su haifi diya mãsu taimakonsa jihãdi fi sabilillahi, amma ya manta, bai ce in Allah Yã so ba. Sai ya sãdu da su, ba su yi cikin ba, sai guda ɗaya daga cikinsu, kuma ta haife shi bãbu rai. Ma'anar kissar, ita ce ko aikin Allah, sai mutum ya mayar da yinsa ga mashĩ'ar Allah, sa'an nan zai ci nasara a kansa.